rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ghana Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugabannin duniya na halartar jana'izar Kofi Annan

media
Uwargidan Kofi Annan, Nane Maria Annan tare da jama'a a wurin bikin jana'izar marigayin ©Reuters/Francis Kokoroko

Shugabannin kasashen duniya da sarakuna da dama na halartar jana’izar tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan a kasar Ghana.


Ana bikin jana'izar ne bayan Ghana ta shafe kwanaki uku tana zaman makokin rashin tsohon jakadan na duniya da ya rasu yana da shekaru 81 bayan fama da gajeran rashin lafiya a gidansa na Switzerland.

Daga cikin masu halartar jana’izar sun hada da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres da shugabannin kasashen Cote d’Ivoire da Liberia da Namibia da Habasha da Nijar da kuma Zimbabwe masu makwabtaka da Ghana.

Ana kuma saran tsoffin shugabannin kasahsen Jamus da Mauritius su halarci bikin jana’izar.

Tuni al’ummar Ghana ta yi bankwana cikin karrama da gawar marigayin.

Kofi Annan ya jagoranci Majalisar Dinkin Duniya tun daga shekarar 1997 zuwa 2006 kuma shi ne mutun na farko daga yankin Afrika da ke kudu da sahara da ya fara rike mukamin.