rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Philippines Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mahaukaciyar guguwa na dab da afka wa Philippines

media
Mutane miliyan biyar na fuskantar barazanar wata mahaukaciyar guguwa a Philippines AFP / Charism SAYAT

Mutane miliyan biyar a Philippines na fuskantar barazanar mahaukaciyar guguwar "Mangkhut" da ke gudun kilomita 255 a cikin sa’a guda.


Rahotanni na cewa, yanzu haka guguwar na tattaro iska kafin ta afka wa yankin arewacin tsibirin Luzon a gobe Asabar.

Tuni aka soke zirga-zirgar jiragen sama da rufe makarantu, yayin da sojoji ke cikin shirin bada agajin gaggawa.

Hukumomin kasar sun gargadi cewa, da yiwuwar guguwar mai tafe da ruwan sama ta haddasa ambaliyar ruwa da zabtarewar laka.

Kasar Philippines na shiga cikin mawuyacin hali da zaran guguwa ta afka ma ta, in da a shekarar 2013, ibtila’in ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 7 tare da jefa miliyoyi cikin kunci.