rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka WHO Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masana na duniya na kokarin ganin bayan cutar tarin fuka nan da shekara ta 2030

media
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres AFP/Florent Vergnes

Kasashen dake cikin Majalisar Dinkin Duniya  sun tsaida shawara don daukan matakan bai daya don yakar cutar tarin fuka, cutar dake sahun gaba wajen hallaka mutane a kasashen duniya.


Bayan da masana cutar suka hana idanuwarsu barci wajen wani taro a New York sun gabatar da tsari na gari da ake sa ran a zartas dashi a babban taro na duniya game da wannan cuta wanda za’a yi a ranar 26 ga wannan wata da muke ciki.

A wajen taron ake sa ran yanke shawarar yin bankwana da cutar a fadin duniya nan da shekara ta 2030.