Isa ga babban shafi
Amurka-China-Rasha

Amurka ta kakabawa China takunkumi saboda sayan makamai daga Rasha

Amurka ta kakabawa China takunkumi kan sayen makamai masu linzamen da jiragen yaki da ta yi daga kasar Rasha, wannan kuma ya kara harzuka kasashen Rasha da Chanar kan yadda Amrukar ke ci gaba da kakaba masu takunkumai.

Tutar Amruka da China
Tutar Amruka da China REUTERS/Damir Sagolj/
Talla

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta saka takunkumin kan kamfanin kera makaman tsaron kasar china sakamakon sayen jiragen yaki samfurin SU-35 da makamai masu linzami samfurin S-400. Da tayi ne daga kasar Rasha

Jami’ai sun ce wannan ne karo na farko da wata kasa ke shan takunkumi, karkashin dokar nan ta dakile ayyukan abokan gaban Amurka,sakamakon dasawa da Rasha, wadda kuma ke nuni da cewa, dangantaka tsakanin gwamnatin shugaba Trump da sauran kasashe na samun cikas.

Sun kuma bayyana cewa mai yiwuwa ne Amurkan ta dau irin wannan mataki, kan duk wata kasa da ta sayi jiragen yaki da makamai masu linzami a hannun Rasha.

Yanzu haka dai Turkiyya, dake da alaka da Amurka na cikin tattaunawa da Rasha kan sayen jiragen da makamai masu linzami.

To sai dai wani babban jami’i a ma’aikatar harkokin wajen Amurka, da ya bukaci sakaya sunansa, ya ce kasar da ake nufi da wannan takunkumi ita ce kasar Rasha.

Ita dai wannan doka ta dakile abokan gaban Amurka ta hanyar takunkumai, an yi ta ne a shekarar 2017, don baiwa gwamnatin shugaba Trump wata kafa ta dankwafe Rasha, Iran, da Koriya Ta Arewa da takunkumai na tattalin arziki da siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.