Isa ga babban shafi

Jirgin agajin Aquarius ya shiga tsaka mai wuya

Kasar Panama ta sanar da kwace lasisin zirga-zirgan a gabar ruwanta ga jirgin agajin Aquarius, sakamakon rashin bin ka’idodin kasa-da-kasa dangane da aikin ceton bakin haure a tekun Mediterranean.

Wasu daga cikin bakin haure da aka ceto kenan da jirgin agajin Aquarius
Wasu daga cikin bakin haure da aka ceto kenan da jirgin agajin Aquarius REUTERS/Guglielmo Mangiapane
Talla

Mahukuntan Panama sunce a shirye suke saf domin kwace tutar kasar su daga jirgin Aquarius, wanda kungiyoyin agaji na likito Medicins sans Frontieres da na SOS Mediterranean ke tafiyar da shi, wajen ayyukan ceto a tekun Baharrum, kuma idan hakan ya kasance, abune mai wuya jirgin ya ratsa gabar ruwan kasar.

Hukumomin Panama dai suka ce, matakin ya samo asali ne sakamakon korafi daga kasar Italiya na cewar, kaftin din jirgin ya ki amincewa da shawarar maida bakin da aka ceto zuwa gabar ruwan kasashen su na asali, wanda acewar su hakan ya saba dokokin kasa-da-kasa.

A nasu bangaren masu tafiyar da wannan jirgin agajin na Aquarius, maida wadanda aka ceto a teku kasashen su na asali, ya saba dokokin kasa-da-kasa, don kuwa dokokin da aka tanada, kan duk wani da aka tsirar a teku, batare da la’akari da yankin da ya fito ko matsayin sa ba, ya zama dole a kai shi ga tudun- mun tsira, kuma kasar Libiya bata daya daga cikinsu, a kiyasin da hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya tayi.

Yanzu haka dai jirgin ya kwashe tsawon kwanaki 19, a tashar ruwan Marseille na kasar Faransa, bayan da aka kore shi a tsibirin Gibralta, inda hukumomin kasar suka ce, Aquarius bai mallaki lasisin ayyukan ceto ba, hasalima jirgi ne, na ayyukan binciken kimiyyan a teku.

Bugu da kari, idan haka ta tabbata, jirgin daya tilo dake ceton rayukan bayin Allah a tekun Mediterranean, na iya kasancewa tamkar jirgin fashin teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.