Isa ga babban shafi
Amurka

Shugabannin kasashen duniya sun gana kan sauyin yanayi

Shugabannin Kasashen Duniya sun gudanar da taro a wani kasaitaccen Otel da ke birnin New York da zummar farfado da yarjejeniyar dumamar yanayi ta birnin Paris da shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga cikinta.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron na kokarin ganin an aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris
Shugaban Faransa Emmanuel Macron na kokarin ganin an aiwatar da yarjejeniyar sauyin yanayi ta birnin Paris REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Taron mai taken ‘Duniya Guda, shi ne irinsa na biyu da aka gudanar tun bayan da shugaban Faransa Emmanuel Macron da wani gungun shugabanni suka kaddamar da shi a bara da nufin gaggauta aiwatar da yarjejeniyar birnin Paris mai cike da tarihi da aka cimma a shekarar 2015.

A shekarar da ta gabata ne, shugaba Macron ya shaida wa takwarorinsa na duniya cewa, lallai basa samun nasara a yakin da su ke yi da matsalar sauyin yanayi, yayin da ya bukaci gaggauta daukan matakan da suka dace.

An shafe watanni 10 da fitar da wasu jerin sanarwa daban daban da kuma gudanar da taruka iri-iri da suka hada da wadanda aka gudanar a biranen Bonn da Bangkok da San Francisco, amma har yanzu babu wani abin kirki da aka tabuka game da yaki da matsalar.

Sakatariyar Yaki da Sauyin Yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya, Patricia Espinosa ta ce, kasashen duniya basa yunkurawa don cika alkawuran da suka dauka kan wannan matsalar.

Taron na baya-bayan nan da shugabannin suka gudanar a birnin New York na zuwa ne a lokaci guda da babban taron Majalisar Dinkin Duniya kuma ya gudana ne a kasaitaccen Otel din nan na Plaza da Donald Trump ya saya a shekarar 1988 akan sama da Dala miliyan 400 kafin ya sayar da shi a shekarar 1995 ba tare da samun riba ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.