Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ya baiwa FBI umarnin bude sabon bincike kan Kavanaugh

Shugaban Amurka Donald Trump ya baiwa hukumar FBI umarnin ta gudanar da sabon bincike akan zargin yunkurin cin zarafi ta hanyar yin fyade, da ake yiwa Brett Kavanaugh, mutumin da yake neman majalisar dattijan kasar ta amince da shi a matsayin babban alkalin kotun kolin kasar.

Brett Kavanaugh yayinda yake kare kansa daga zargin cin zarafin mata a zauren majalisar dattijan Amurka.  27 ga Satumba, 2018.
Brett Kavanaugh yayinda yake kare kansa daga zargin cin zarafin mata a zauren majalisar dattijan Amurka. 27 ga Satumba, 2018. Win McNamee/Pool via REUTERS
Talla

kafin bayar da wannan sabon umarnin dai, an shafe dogon lokaci ana tafka muhawara a majalisar dattawan ta Amurka dangane da kada kuri'ar amincewa da zabin shugaban na Amurka, na jagorancin kotun kolin kasar.

Ana dai zargin Brett Kavanaugh da yi kokarin aikata laifin fyade kan wata mata a lokacin da yake matashi dan shekaru 17 a duniya.

A halin da ake ciki, shugaban kwamitin majalisar dattijan dake tantance Kavanaugh Chuck Grassley, ya amince da jinkirta kada kuri'ar karshe zuwa mako guda, akan tabbatar da Kavanaugh a matsayin jagoran alkalin kotun Amurka ko akasin haka.

Zuwa yanzu dai mata uku ne suka bayyana cewa Kavanaugh mai shekaru 53 ya ci zarafinsu a lokacin da yayi tatul da barasa yayinda yake matashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.