Isa ga babban shafi
Falasdinu

Falasdinawa sun gurfanar da Amurka gaban kotun duniya

Kotun duniya, ta ce Yankin Falasdinu ya shigar da karar Amurka a gabanta, dangane da matakin da ta dauka, na sauya mazaunin ofishin jakadancinta daga Tel Aviv zuwa Birnin Kudus.

Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da matarsa Sara Netanyahu yayin ziyarar ofishin jakadancin Amurka da ya koma Birnin Kudus. 14 ga watan Mayu, 2018.
Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da matarsa Sara Netanyahu yayin ziyarar ofishin jakadancin Amurka da ya koma Birnin Kudus. 14 ga watan Mayu, 2018. REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Yankin na Falasdinu ya ce matakin wanda ya nuna amincewar Amurka karara kan mayar da Hedikwatar Isra’ila zuwa Birnin na Kudus, ya sabawa dokokin duniya, inda yankin ke neman kotun ta tilastawa Amurka janye ofishin nata daga birnin.

A watan Disambar bara shugaba Donald Trump ya bada umarnin aiwatar da sauya mazaunin ofishin jakadancin Amurka zuwa Birnin Kudus daga Tel Aviv, wanda ya soma aiki a watan Mayu da ya gabata.

Majalisar Dinkin Duniya ta kafa kotun duniya ta ICJ ce domin warware rikici tsakanin kasashe, kuma a shekarar 2012 zauren Majalisar Dinkin Duniyar ya amince da yankin Falasdinu a matsayin mai sa ‘ido kan al’amuran kotun, amma wanda bashi da kujera a cikinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.