Isa ga babban shafi
China

Interpol ta tuhumi China kan bacewar shugabanta

Hukumar ‘yan sandan duniya Interpol ta bukaci gwamnatin China ta yi mata cikakken bayani, akan inda shugabanta Meng Hongwei yake, wanda aka nema sama da kasa aka rasa, jim kadan bayan isa kasar.

Shugaban Hukumar 'Yan Sandan Duniya, Meng Hongwei.
Shugaban Hukumar 'Yan Sandan Duniya, Meng Hongwei. ROSLAN RAHMAN / AFP
Talla

Da fari dai wasu rahotanni sun ce, jami’an tsaron kasar ta China ne suka kame tare da tsare shugaban ‘yan sandan na Interpol domin yi masa tambayoyi dangane da zargin aikata almundahana da ake masa.

Kafin zama shugaban Interpol a shekarar 2016, Meng ya rike mukamin mataimakin Minista Tsaron Al’umma a kasarsa China.

To sai dai har yanzu China bata ce komai ba dangane da zargin da ake mata na hannu wajen batan Meng Hongwei, wanda ganin da aka yi masa na karshe, shi ne lokacin da ya bar hedikwatar rundunar ‘yan sandan ta duniya dake birnin Lyon na Faransa domin zuwa mahaifarsa kasar China.

Tuni dai rundunar ‘san sandan Faransa ta kaddamar da bincike game da bacewar shugaban Hukumar ‘yan sandan Kasa da Kasa, Meng Hongwei, wanda shi ne mutun na farko daga kasar China da ya rike wannan mukami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.