Isa ga babban shafi
Brazil

Bolsonaro ya lashe zagayen farko na zaben Brazil

Sakamako zaben shugaban kasar Brazil ya nuna cewar, dan takarar jam’iyyar 'yan ra’ayin rikau, Jair Bolsonaro ya lashe zagayen farko na zaben, in da ya yi zargin cewar magudi ne ya hana shi samun nasara kai tsaye, abin da zai kai ga zuwa zagaye na biyu nan da makwanni uku masu zuwa.

Jair Bolsonaro ya yi zargin tafka magudi a zaben don hana shi zama shugaban kasa kai tsaye
Jair Bolsonaro ya yi zargin tafka magudi a zaben don hana shi zama shugaban kasa kai tsaye EVARISTO SA / AFP
Talla

Bolsonaro mai shekaru 63, wanda tsohon sojin lema ne, ya sha alwashin murkushe masu aikata laifuffuka a babbar kasar da ke yankin Amurka ta Kudu, abin da ya ba shi nasarar samun kashi 46 na kuri’un da aka kada, wanda ya gaza sama da kashi 50 da ake bukata kai tsaye ya zama shugaban kasa.

Wannan sakamako ya nuna cewar, Bolsonaro zai sake karawa da Fernando Haddad ranar 28 ga wata, saboda shi ya zo na biyu da kashi 28.

Haddad dai tsohon Magajin Garin Birnin Sao Paulo ne, wanda ya maye gurbin shugaba Inacio Lula da Silva da aka haramta wa tsayawa takara saboda daurin da aka masa a gidan yari.

A wani labari kuma, tsohuwar shugabar kasar da aka tilasta wa sauka daga mulki, Dilma Roussef ta gaza wajen lashe kujerar Majalisar Dattawa, saboda yadda ta zo ta 4 da kashi 15 kacal na kuri’un da aka kada a Jihar Minas Gerais.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.