rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Sufuri

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 20 sun mutu a haadarin mota a Amurka

media
An killace wurin da hadarin ya auku a birnin New York cbsnews.com

Akalla mutane 20 ne aka tabbatar da mutuwarsu sakamakon wani hadarin mota a birnin New York na Amurka, lokacin da wata mota kirar limousine ta kwace daga hannun matukinta, ta kuma abka wa jama’a.


Mataimamin Sufritandan 'Yan Sanda, Christopher Fiore ya ce, daukacin mutane 18 da ke cikin motar sun mutu, yayin da wasu biyu daban da ke tafiya a kasa su ma suka rasa rayukansu.

Hukumar Kula da Hadura ta New York ta hannun shugabanta, Robert Sumwalt, ta ce wannan shi ne mafi munin hadarin da suka gani a cikn 'yan shekarun nan.

Rahotanni na cewa, mutanen da ke cikin motar na kan hanyarsu ce ta zuwa biki, yayin da Hukumar Kula Hadduran, ta aika wata tawaga ta musamman don gudanar da bincike a wurin da lamarin ya faru.