rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Guguwar Michael ta yi barna a Amurka

media
Guguwar Michael ta tubuke bishiyoyi da turaken wutar lantarki a Florida REUTERS/Steve Nesius TPX IMAGES OF THE DAY

Mazauna jihar Florida ta Amurka sun wayi gari a yau Alhamis cikin alhini bayan guguwar da aka yi wa lakabi da Michael ta yi barna tare da hallaka akalalla mutane biyu.


Unguwannin da ke birnin Panama sun cika makil da karyayyun bishiyoyi da turaken wutar lantarki da rufin gidaje da suka rikito har ma da tarwatsattsun gilasai da sauran buraguzai bayan wucewar guguwar ta Micheal wadda aka bayyana a matsatun mafi muni da ta afka wa Amurka tun shekarar 1969.

Gwamnan Jihar Florida, Rick Scott ya shaida wa kafar talabijin ta CNN cewa, guguwar ta yi matukar barna, in da ya ce, babbar damuwarsa ita ce, asarar rayukan da aka samu.

A cewar Gwamna Scott wanda ke shirin ziyartar yankin da abin ya auku, sun samu labarin jikkatar dimbin jama’a.

Yanzu haka dai, kwararru na cewa, guguwar mai dauke da iska ta rage karfinta bayan gudun da ta yi na kilomita 250 cikin sa’a guda.

Bayan gilmawarta a Florida, guguwar ta doshi hanyar Alabama da Georgia da kuma Kudancin Carolina.

Guguwar ta tunbuke manyan alluman tallace-talace da aka dasa a Alabama, yayin da aka kwashe su daga kan hanya don bai wa motoci damar wucewa a safiyar yau.

A yayin zantawa da kafar Fox, shugaban Amurka Donald Trump ya yi alkawarin cewa, za su gaggauta sake gina yankunan da guguwar ta yi ta’adi.