Amurka ta soke takardun shiga kasar na wasu jami`an Saudiya
Amurka ta sanar da janye takardun shiga kasar da wasu mutane da ake zargin suna cikin wadanda suka kashe fitaccen dan jaridan Saudiya Jamal Kashoggi, a birnin Santambul na Turkiya.
Wallafawa ranar:
Tun bayan da Saudiya ta amsa laifin kisan dan jaridan ne kasashen Duniya suka soma nuna damuwa tareda bukatar samun Karin haske dangane da kisan dan jaridan.
Mike Pompeo sakataren waje na Amurka ya bayyana cewa Amurka ta gamo mutane kusan dozen biyu dake da hannun wajen kisan dan jaridan.
Yace Amurka za ta kara daukan matakan hukunta mutanen da aka gano.
Yarima Ben Salmane ya dau alkawalin bayar da goyan baya zuwa ga masu bincike don gano gaskiyar abinda ya faru dangane da kisan dan jaridan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu