rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
  • Palestinawa 22 hare-hare daga Israela ya kashe a Gaza.
  • Dan kunar bakin wake ya kashe mutun daya a ofishin 'yan sandan Indonesia
  • Yau ake zama a bainin jama'a game da tsige Shugaban Amurka Trump
  • Wasu 'yan kasar Kamaru sun shiga Otel da Shugaba Paul Biya ke ciki a Paris.
  • Tashin Bam a Kabul na Afghanistan ya kashe mutane 7
  • Saudiya, Daular Larabawa da Bahrain za su shiga wasannin kwallon kafa tare

Amurka Donald Trump Barack Obama Hillary Clinton

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta kaddamar da bincike kan sakwannin bama-bamai

media
Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama da Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Wajen kasar Hillary Clinton na cikin wadanda aka aika wa da sakwannin bama-baman REUTERS/Mike Segar

Gwamnatin Amurka ta kaddamar da bincike game da kunshin sakwannin da ke dauke da bam da aka aika wa manyan jami’an gwamnatin kasar na da da yanzu.


Daga cikin wadanda aka aika wa sakon har da Tsohon Shugaban kasar, Barack Obama da Tsohuwar Sakatariyar Harkokin Waje, Hilary Clinton.

Tuni shugaba Donald Trump ya bukaci hadin kan al’ummar kasar ganin yadda al’amarin ya shafi manyan jagororin jam’iyyar Democrat mai adawa.

A yayin gabatar da jawabi a fadar White House, shugaba  Trump ya ce, a wannan lokaci ya kamata su hada kansu wuri guda don nuna wa duniya cewa, rikicin siyasa ko wanne iri ba shi da wurin zama a Amurka.

"Samar da tsaron al’ummar Amurka shi ne babban abin da na sa a gaba, yanzu na kammala ganawa da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta FBI da Hukumar Shari’a da Hukumar Tsaron Cikin Gida, da kuma Hukumar Leken Asiri" in ji Trump.

Shugaban ya kara da cewa "A yanzu yadda muke magana, kwararrun jami’an kwance bama-bamai na gudanar da bincike kan wadannan sakwanni masu dauke da abubuwan fashewa, kuma gagarumin binciken gwamnatin tarayya na nan tafe."

A yayin mayar da martani jim kadan da gano wadannan bama-bamai Hilary Clinton ta ce, "Lokaci ne na damuwa, lokaci ne na rarrabuwan kawuna, dole ne mu yi duk mai yiwuwa don hada kan kasarmu, dole ne mu zabi shugaban da shi ma zai aiwatar da haka."

Kafar Watsa Labarai ta CNN na daga cikin wadanda aka aike wa da irin wannan sako mai dauke da bam.