Isa ga babban shafi
Jamus-Afrika

"Ku mayar da hankalinku Afrika saboda arzikin nahiyar"

Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci kamfanonin kasar ta da su karkata akalar harkokinsu daga nahiyar Asiya zuwa Afrika saboda arzikin da Allah Ya wadata nahiyar da shi. Merkel ta bayyana fatar matakin zai magance matsalar kwararar bakin a Turai.

Shugabar Gwamnatin Jamus Merkel tare da Firaministan Habasha Abiy Ahmed a taron zuba jari da  kasashen Afrika suka halarta a birnin Berlin
Shugabar Gwamnatin Jamus Merkel tare da Firaministan Habasha Abiy Ahmed a taron zuba jari da kasashen Afrika suka halarta a birnin Berlin REUTERS/Hannibal Hanschke
Talla

Yayin da take jawabi wajen taron zuba jari a birnin Berlin wanda ya samu halartar wasu shugabannin kasashen Afrika da suka hada da Firaministan Habasha, Abiy Ahmed da na Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa da shugaban Rwanda Paul Kagame, Merkel ta ce, sun dade suna mayar da hankali kan harkokin kasuwanci da zuba jari a nahiyar AsiYa, saboda haka lokaci ya yi da za su karkata akalarsu zuwa AfrIka.

Shugabar Gwamnatin ta ce, kasashen Turai suna maraba da yanayin zuba jari mai kyau da yanzu haka ake samu a wasu kasashen Afrika, wanda zai bada damar zuba jarin gwamnati da na 'yan kasuwa.

Merkel ta ce, shirin nasu zai bada damar taimaka wa kasashen Afrika wajen zuba jarin kamfanoni da kuma amfana da fasahohin ci gaba, yayin da ake bukatar kasashen su aiwatar da sauye-sauyen da za su inganta hanyoyin zuba jari wajen yaki da cin hanci da kuma tabbatar da aiki da doka.

Yayin jawabinsa, shugaba Kagame ya yaba da matakan da kamfanonin Volkswagen da Siemens suka dauka wajen bude rassa a Rwanda wanda ya ce, tuni sun bude kofa ga wasu takwarorinsu.

Tuni kasashen Ghana da Cote d’Ivoire suka karbi tallafin da ya kai Euro miliyan 365 daga kasar ta Jamus.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.