Isa ga babban shafi
Jamus-Lafiya

"Na kashe marasa lafiya 100 a asibiti"

Wani tsohon ma'aikacin jinya  a Jamus, ya amince da kisan marasa lafiya har guda 100 a yayin da aka fara tuhumar sa a ranar Talata, abin da ya sa ya zama daya daga cikin mutanen da suka fi kisa akai akai a duniya.

Niel Hogel ya rufe fuskarsa don kauce wa daukar hoton Kamara
Niel Hogel ya rufe fuskarsa don kauce wa daukar hoton Kamara Reuters
Talla

Jami’an bincike sun bayyana cewa, Niels Hogel mai shekaru 41, ya dirka wa mutanen da ke karkashin kularwarsa magungunan da suka wuce kima a wasu asibitoci biyu da ke arewacin Jamus.

Koda yake masu shigar da kara sun ce, manufar Hogel ita ce, birge abokan aikinsa ta hanyar gaggauta farfado da marasa lafiyar da ya dirka wa magungunan.

Tuni Hogel ya fara zaman daurin rai da rai bisa kisan wasu majinyata shida da ke karkashin kulawarsa.

Rahotanni na cewa, ya kashe akalla marasa lafiya 36 a Oldenburg da kuma 64 a kusa da Delmenhorst tsakanin shekarar 1999-2005.

Sabuwar tuhumar da aka fara yi masa za ta kai har cikn watan Mayu kuma an kaddamar da ita ne bayan tsawon shekarun da aka kwashe na gwajin guba kan gawarwakin mutane 130 da aka tono su daga kaburbura.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.