rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yau ce ranar yaki da cin zarafin yan jaridu ta duniya

media
yan uwa da aminan arizikin Ghislaine Dupont da Claude Verlon ke nan ke zanga zangar neman samar da haske kan kisan da aka yi masu (nan sun taru ne 2017). BERTRAND GUAY / AFP

A yau juma’a 2 ga watan Nowamba ne, Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar yaki da galazawa yan jarida ta Duniya.

Samar da wannan rana dai, ya biyo bayan kisan da yan ta’adda suka yi wa wasu yan Jaridu Radio France Internationale RFI ne su biyu mace da namiji Ghislaine Dupont da Claude Verlon a Kidal da ke arewacin kasar Mali a ranar 2 ga watan nowambar 2013.


Kasashen dunya, kungiyoyin kare hakin yan jaridu da dama, na ke ci gaba da bayyana damuwa kan yadda ake ci gaba da kisa tare da galazawa yan jaridu a Duniya.

Kisan baya bayan nan da aka yi wa dan jarida, shine na Jamal Kashoggi da ake zargin yarima mai jiran gadon kasar Saudiya Mahamed bin Salman da kitsawa a cikin ofishin jakadancin kasar ta Saudiya dake Istanbul a kasar Turkiya.

A wannan karo an shirya bikin ne a kasar Cote D`ivoire wanda zai samun halartar manyan masu fada aji, Shugabanin kungiyoyin yan jarida da kare hakkin dan adam a duniya.

Sakamakon wannan rana dai sashen faransanci na Redio France International RFI ya wata tattauanwa da tsohon Shugaban Faransa Francois Hollande dake shugabancin faransa a lokacin da aka aikata kisan yan jaridu a Kidal dangane da irin matakan da gwamnatinsa ta dauka a wancan lokaci.

A yau tashoshin yada labaran Faransa da suka hada da Radiyo RFI, France 24, Monte Carlo Doualiya, za su gabatar da shirye shirye na musaman kan ranar, da kuma baiwa daliban kasar Cote d`ivoire da suka shiga wata gasa ta samun tallafi da kuma horon da ake yiwa lakabi da kyautar Ghislaine Dupont da Claude Verlon na wannan shekara kan sanin makamar aiki jarida a tsanake.