rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka ta hukunta Sojinta da ke tawagar wadanda aka kashe a Nijar

media
Babban mashawarcin Amurka kan harkokin tsaro John Bolton. REUTERS/Maxim Shemetov

Rundunar Sojin Amurka ta ladabtar da wasu jami’an ta guda 6 saboda rawar da suka taka wajen kuskuren da ya faru a Jamhuriyar Nijar bara wanda ya yi sanadiyar kashe sojojin kasar guda 4 tare da na Nijar guda 5.


An dai samu matsalar ne ranar 4 ga watan Oktobar bara, lokacin da wata tawagar sojojin Amurka guda 12 tare da na Nijar guda 30 suka gamu da kwantan bauna a Tongo Tongo yayin da su ke dawowa daga wani aiki kusa da iyakar Mali.

Cikin wadanda aka ladabtar sun hada da Kaftin Mike Perozini, shugaban tawagar zaratan sojojin da mataimakin sa.

Jaridar New York Times ta ce an samu jami’an ne da rashin nuna kwarewa lokacin gudanar da aikin, abinda ya kai ga kashe jami’an su.