rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa za ta tallafawa Africa ta tsakiya da Yuro Miliyan 24

media
Shugaban Janhuriyar Tsakiyar Afrika Faustin-Archange Touadéra rfi

Kasar Faransa ta yi alkawarin bai wa kasar Janhuriyar Tsakiyar Afrika tallafin kudi Euro miliyan 24 da kuma wasu makamai na yaki ga wannan kasa wadda renon Faransan ce.


Ministan Waje na Faransa Jean-Yves Le Drain ya shaidawa manema labarai haka a Bangui bayan da ya gana da Shugaban kasar Janhuriyar Tsakiyar Afrika Faustin-Archange Touadera.

Ministan waje na Faransa ya sanya hannu cikin wata yarjejeniya don biyan albashin albashi da kudaden ajiye aiki da maaikata ke bin Gwamnati da wasu ayyukan samar da gadoji da hanyoyi.

Yace Faransa nan bada dadewa ba za ta samar da bindigogi 1,400 ga sojojin Janhuriyar Afrika ta Tsakiya.