Isa ga babban shafi
Iran-China

China ta sha alwashin ci gaba da kasuwanci da Iran

China ta bayyana aniyar ta na cigaba da hada hadar kasuwanci da kasar Iran, bayan yin Allah wadai da takunkumin da Amurka ta dorawa kasar.Matakin na China na zuwa a dai dai lokacin da shugaban kasar ta Iran Hassan Rouhani ke shan alwashin karya takunkuman na Amurka.

Shugaban kasar China Xi Jinping.
Shugaban kasar China Xi Jinping. ©REUTERS/Aly Song
Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Hua Chunying, ya ce China bata goyan bayan takunkumin da Amurka ta yi gaban kan ta wajen dorawa Iran, saboda haka za su cigaba da hulda da kasar kamar yadda dokokin duniya suka tanada.

Tuni kasashen Faransa da Jamus da Birtaniya da Rasha da kuma kungiyar kasashen Turai suka bayyana adawar su da takunkumin, yayin da suka bayyana samar da wata hanyar cinikayya da kasar da kasar ta Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.