rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Iran Amurka Nukiliya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Iran ta lashi takobin karya takunkuman Amurka

media
Shugaban Amurka Donald Trump tare da Hassan Rouhani na Iran HO, Nicholas Kamm / AFP / IRANIAN PRESIDENCY

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya lashi takobin karya tsauraran takunkuman da Amurka ta sake malkaya mata da zummar gurgunta bangaren tattalin arzinta.


Gwamnatin shugaba Donald Trump ta maido da dukkanin takunkuman da aka dage wa Iran a karkashin yarjejeniyar nukiliyarta a shekarar 2015.

Takunkuman za su shafi bangaren fitar da man fetir zuwa kasashen ketare da harkokin zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma hada-hadar bankuna, yayin da kasashe za su fuskanci tsanani wajen huldar kasuwanci da Iran mai arzikin man fetir.

Sai dai a yayin wani taro da hukumomin tattalin arzikin kasar, shugaba Rouhani ya yi wasti da takunkuman, in da ya ce, Iran za ta ci gaba da hada-hadarta ta sayar da man fetir.

Kasashen Turai sun ce, za su taimaka don ganin harkokin kasuwanci sun kauce wa fuskantar takunkuman na Iran, amma ana shakku game da matakan da za su dauka don cimma wannan buri.

A farkon shekarar nan ne, shugaba Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran bayan ya bayyana ta a matsayin mafi muni a tarihi.