Isa ga babban shafi
Turkiya-Saudiya

Turkiya ta zargi Saudiya da goge duk wata hujja kan kisan Khashoggi

Kasar Turkiya ta zargi Saudi Arabia da tura wata tawagar mutane biyu birnin Santanbul domin batar da duk wata shaida da ake da ita dangane da kisan gillar da aka yi wa Jamal Khashoggi a ofishin Jakadancin ta.

Ka zalika Erdogan ya nesanta sarki Salman a matsayin wadanda ya yi umarnin kisan ko kuma ya ke da masaniya kan kisan, sai dai ya ce babu shakka wani da ke da ikon fada aji a kasar ne ya bada umarnin.
Ka zalika Erdogan ya nesanta sarki Salman a matsayin wadanda ya yi umarnin kisan ko kuma ya ke da masaniya kan kisan, sai dai ya ce babu shakka wani da ke da ikon fada aji a kasar ne ya bada umarnin. 路透社。
Talla

Wani jami’in gwamnatin Turkiya ya bayyana cewar mutanen biyu da aka tura kasar kafin barin Yan Sanda su gudanar da bincike a ofishin Jakadancin Saudiyan na birnin Santanbul, sun je ne kawai domin batar da duk wata shaida da za a iya samu kan kisan fitaccen dan jaridar.

Jami’in ya kuma tabbatar da rahotan Jaridar Sabah da ke cewar masana kimiyya Ahmad Abdelaziz al-Janobi da Khaled Yahya al-Zahrani na daga cikin wadanda aka tura Turkiyar domin lalata shaidun da ake da su.

A wasu jawaban shugaba Erdogan na baya-bayan nan kan kisan Jamal Khashoggi, shugaban ya ce an gudanar da kisan a tsare kuma karkashin umarni daga wani kusa a masarautar Saudiyan.

Ka zalika Erdogan ya nesanta sarki Salman a matsayin wadanda ya yi umarnin kisan ko kuma ya ke da masaniya kan kisan, sai dai ya ce babu shakka wani da ke da ikon fada aji a kasar ne ya bada umarnin.

Jamal Khashoggi dai fitaccen dan jarida ne da ke rayuwa a gidan sarautar ta Saudiya ya kuma san siriin gidan kafin samun sabaninsu da ya kai shi ga yin kaura zuwa Turkiya.

Rahotanni sun ce gidan sarautar a Lokuta da dama ya bukaci Khashoggi ya dawo gida amma dan jaridar yaki amincewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.