rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jam'iyar demokrat ta samu rinjaye a majalisar wakilan Amurka

media
layin masu zaben tsakkiyar wa'adi a kasar Amruka 6 nowamba 2018 REUTERS/Joe Skipper

Jam’iyar demokrat a kasar Amruka ta samu gagarumar nasara a zaben tsakiyar wa’adin da aka gudanar a jiya talata, inda ta lashe kusan daukacin kujerun majalisar wakilan kasar. A nata bangaren Jam’iyar Republican ta yi nasarar rike rinjayen da take da shi a majalisar dattawa, wanda shugaba Donald Trump ya bayyana a matsayin gagarumin ci gaba, ba tare da yin tsokaci ga koma bayan da jami’iyarsa ta cimma a majalisar wakilan kasar ba.


Wannan nasara da jam’iyar demokrat ta samu dai, na iya haifarwa shugaban na Amruka tarnaki har zuwa karshen wa’adinsa na shekara ta 2021.

Shekaru 2 bayan nasarar da dan kasuwar ya samu na zama kan kujerar shugabancin fadar Wit house ta Amruka ba tare da wata cikkiyar kwarewa ta siyasa ko diflomasiya ba, a jiya talata 6 ga watan nobemba amerikawa sun halarci rumfunan zabe da himma saboda matukar muhimmancin da yake da shi a kasar, da kuma kan siyasar tattalin arzikin da shugaba Donald Trump ga kasashen duniya

A cewar hasashen da kafofin talabijin din kasar Amruka suka yi, jam’iyar Republican ce ta lashe rinjayen majalisar wakilan kasar a karo na farko tun bayan 2010. A yayinda a nata bangaren jam’iyar Republican ke ci gaba da rike rinjayenta a majalisar dattawa bayan haka ma ta samu karin kujreru 2 a zaben

A watan janairun 2019 mai zuwa Amurka za ta fara aiki majalisar wakilan ta 116 a tarihi da kuma ke fuskantar rarrabuwar kanu, a cikin al’ummar dake da baraka kan shugaba Donald Trump

zaben na tsakiyar wa’adi dai a al’adance ya kan kasance mai wahala ga shugaban dake ci a kan karaga a kasar Amruka.

To sai dai rasa rinjayen majalisar wakilai, duk kuwa da ci gaba mai armashi da aka samu ta fannin bunkasuwar tattalin ariziki da kasar ta samu, wani koma baya ne ga shugaba dan kasuwar gidaje, a zaben da ake dauka a matsayin gagarumin zaben raba gardama kan makomar shugaban kasar Donald Trump