rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Zaben Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An zabi mata Musulmai a Majalisar Amurka

media
Rashida Tlaib da Ilhan Omar mvslim.com

A karon farko a tarihin Amurka, an zabi mata biyu Musulmai don wakiltan jihohinsu a zauren Majalisar wakilan kasar.

 


Ilhan Omar da Rashida Tlaib, sun lashe kujerunsu a karkashin inuwar jam’iyyar Democrat.

Omar da iyayenta suka yi hijira daga Somalia ta samu nasarar zama ‘yar Majalisa daga jihar Minnesota, in da za ta maye gurbin Keith Ellison, wanda shi ma kansa Musulmi ne da a can baya aka zabe shi a Majalisar Dokokin Kasar.

A yayin gabatar da jawabi ga dandazon magoya bayanta jim kadan da samun nasarar, Omar ta ce, " Mace ta farko mai launi daban, da za ta wakilci jiharmu a Majalisar Dokoki, mace ta farko mai sanye da hijabi, kuma mace ta farko ‘yar gudun hijira da aka zaba don wakilci a Majalisar Dokokin."

Ita ma Rashida Tlaib wadda aka haifa a jihar Detroit bayan iyayenta sun yi kaura daga Palestine, ta samu nasarar lashe kujerarta ba tare da wata hamayya daga wani dan takarar jam’iyar Republican mai mulki a Michigan.

Ana kallon wannan nasarar ‘yan matan Musulman a matsayin wani gagrumin tarihi, musamman idan aka yi la’akari da cewa, an zabe su ne a dai dai lokacin da Majalisar Kula da Huldar Musulman Amurka ta ce, an samu karuwar ayyukan kyama kan Musulmai a kasar da kashi 21 cikin watanni shida na wannan shekarar.