rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Isra'ila

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dan bindiga ya kashe mutane 12 a Amurka

media
Jami'aan 'Yan Sanda sun killace wurin da al'amarin ya auku Thomas Gorden/via REUTERS

Wani dan bindiga ya bude wuta kan mai uwa da wabi a wani gidan rawa makare da jama’a a Thousands Oak da ke birnin Los Angeles na jihar California ta Amurka, in da ya kashe mutane akalla 12.


Ofishin ‘Yan Sandan yankin ya ce, al’amarin ya faru ne a dai dai lokacin da daliban wata makarantar Kwaleji ke gudanar da biki a cikin daren ranar Laraba.

Rahotanni na cewa, an ga gawar maharin kwance a kasa, amma babu cikakken bayani kan ko shi ya hallaka kansa ko kuma  jami'an 'yan sanda ne suka kashe shi.

Rahotannin sun kara da cewa, akalla an ji harbe-harben bindiga har sau 30 kuma wani jami'in 'yan sanda na cikin wadanda suka rasa rayukansu

Amurka na fama da matsalar hare-haren ‘yan bindiga dadi a kasar, abin da ke lakume rayukan jama’a da dama.