Isa ga babban shafi
Lafiya

Kwayar Cuta za ta kashe miliyoyin mutane a Turai

Miliyoyin mutane a Turai da Amurka za su rasa rayukansu muddin aka gaza shawo kan wata kwayar cuta da ke bujire wa magani kamar yadda kwararru suka yi hasashe.

Talla

Cibiyar Bunkasa Tattalin Arziki ta OECD, ta yi gargadi game da munanan abubuwan da za auku ga bangaren kiwon lafiyar al’umma har sai an inganta tsarin kula da lafiya tare da rage yawaitar amfani da wasu nau’oi’in magunguna.

Wani sakamakon bincike da aka fitar a wannan makon ya ce, magungunan da ke yaki da kwayoyin cutuka sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dubu 33 a shekarar 2015 kadai a kasashen Turai.

A yanzu kuma, cibiyar ta OECD ta ce, ana iya samun mutane akalla miliyan 2.4 da za su iya rasa rayukansu nan da shekarar 2050 sakamakon kwayoyin cutukan masu bujire wa magani.

A cewar cibiyar, kudaden yaki da kwayoyin cutar zai tashi zuwa Dala biliyan 3.5 a kowacce shekara kuma a kowacec kasa.

Babban Jami’i a cibiyar, Michele Cecchi ya ce, ko a yanzu, kwayar cutar na lakume akalla kashi 10 cikin 100 na kasafin bangaren kiwon lafiyar kasashe.

Jami’in ya ce, wannan kwayar cutar na lakume kudade fiye da wandanda ake kashewa wajen yaki da zazzabin murar tsuntsaye da cutar Kanjamau da kuma tarin fuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.