Isa ga babban shafi
Amurka-Ta'addanci

Amurka ta yi sanadin mutuwar mutane dubu 500 - Rahoto

Wani bincike ya nuna cewa yaki da ta’addancin da Amurka ta kaddamar a kasashen Iraqi, Afghansitan da kuma Pakistan, bayan harin 11 ga watan Satumba na shekarar 2001, yayi sanadin kashe mutane 500,000

Wasu sojin Amurka a kudancin kasar Afghanistan.
Wasu sojin Amurka a kudancin kasar Afghanistan. Reuters/Goran Tomasevic
Talla

Rahoton da Jami’ar Brown Waston ta wallafa, yace adadin mutanen da suka mutun ya tashi ne daga dubu 480,000 zuwa dubu 507,000, alkaluman da suka zarce na shekaru biyu da suka gabata da karuwar adadin sama da mutane dubu 110,000 da suka hallaka.

Rahoton ya kara da cewar, tsakanin fararen hula dubu 182,272 zuwa dubu 204,575 aka kashe a Iraqi da sunan yakin, yayin da aka kashe fararen hula dubu 38,480 a Afghanistan da kuma dubu 23,372 a Pakistan.

Binciken yace a bangaren Amurka kuwa, tun bayan kaddamar da yakar ta’addancin, rayukan sojojinta kusan 7,000 ne suka salwanta a Iraqi da Afghanistan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.