Isa ga babban shafi
Duniya

"Yawan al'ummar Duniya zai kai biliyan 10 a 2050"

Wani bincike ya nuna cewar an samu karuwar haihuwa a kasashe masu tasowa, abinda ke nuna karuwar jama’a a duniya, yayin da kuma mata a kasashen dake da dukiya basa haihuwar isassun yaran da ake bukata.

Kididdiga ta nuna cewa yawan al'ummar Duniya a halin yanzu ya kai biliyan 7 da miliyan 600.
Kididdiga ta nuna cewa yawan al'ummar Duniya a halin yanzu ya kai biliyan 7 da miliyan 600. Tom Hilton CC BY 2.0
Talla

Binciken da Cibiyar kula da lafiya da kuma kididdiga ta Jami’ar Washington ta gudanar, wanda Gidauniyar Bill da Melinda Gates suka dauyi, yayi amfani da bayanai sama da 8,000, kuma sama da 600 daga cikin su sabbi ne, wajen rubuta wannan bayanin.

Rahotan yace Cibiyar tayi amfani da binciken da akayi a cikin kasa da dandalin sada zumunta da kuma wasu hanyoyi na daban, wanda ya nuna alkaluman haihuwa da mutuwa da rashin lafiyar dake kashe dubban mutane cikin kowacce kasa, inda aka gano cewar yanzu haka bugun zuciya shi ne kan gaba wajen kisa a duniya.

Binciken ya gano cewar, adadin mutanen dake duniya ya tashi daga biliyan 2 da miliyan 600 a shekarar 1950 zuwa biliyan 7 da miliyan 600 bara.

Binciken ya kuma gano cewar kasashe 91, akasari daga Turai da Arewaci da Kudancin Amurka basa haihuwar yara da yawa, yayin da ake cigaba da samun karuwar haihuwa a Afrika da Asia, inda a Jamhuriyar Nijar mace guda kan haifi akalla yara 7, yayin da ake samun yara 6 a Mali da Chadi da Afghanistan.

Farfesa Ali Mokdad, na Cibiyar kula da lafiyar, yace hanya taya tilo da za’ayi amfani da ita wajen daidaita karuwar jama’a itace bada ilimi.

Majalisar Dinkin Duniya tayi has ashen cewar nan da shekarar 2050 yawan mutanen duniya zai kai biliyan 10, ganin yadda ake samun karuwar haihuwa akasashe maus tasowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.