Isa ga babban shafi
Faransa-Majalisar Dinkin Duniya

Macron, Merkel da Guterres sun yi tir da dabi'ar sabawa dokokin duniya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron da takwarar sa ta Jamus, Angela Merkel da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres sun gargadi kasashen duniya da su kaucewa hadarin da ke tattare da shirin shugaba Donald Trump wanda ya sanya kasar a gaba.

Shugabannin wadanda basu kira sunan Trump karara ba, sun yi Allah wadai da kokarin sabawa dokokin duniya wajen taron zaman lafiyar da Macron ya jagoranta.
Shugabannin wadanda basu kira sunan Trump karara ba, sun yi Allah wadai da kokarin sabawa dokokin duniya wajen taron zaman lafiyar da Macron ya jagoranta. REUTERS/Gonzalo Fuentes/Pool
Talla

Shugabannin wadanda basu kira sunan Trump karara ba, sun yi Allah wadai da kokarin sabawa dokokin duniya wajen taron zaman lafiyar da Macron ya jagoranta.

Yayin jawabi ga taron zaman lafiyar da ya samu halartar shugabannin kasashen duniya sama da 60, Angela Maerkel ta ce tana fargaba kan manufofin 'yan siyasar da ke fifita kasar su, ba tare da la’akari da yadda duniya take ba.

Merkel ta ce irin wannan hali zai shafi makomar zaman lafiya da kuma muradun kasashen duniya, wanda zai iya kaiga sanya alamar tambaya ga muradun zaman lafiyar Turai.

Shi kuwa a na shi jawabi, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci shugabannin na duniya su kaucewa daukar matakan da za su rarraba kawunan jama’a kamar yadda aka gani a shekarar 1930.

Guterres ya bayyana cin diddigen dimokiradiya da kuma sabawa dokokin duniya a matsayin gubar d ake yi wa zaman lafiya barazana.

Shugaba Emmanuel Macron da ya jagoranci taron, tambaya yayi kan yadda duniya za ta tunashugabanni 70 da suka halarci bikin kawo karshen yakin duniya, ta hanyar matakan da suke dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.