Isa ga babban shafi
Faransa-Majalisar Dinkin Duniya

Kasashen Duniya sun sha alwashin yakar hare-haren Intanet

Kasashen duniya 51 da suka hada da na Tarayyar Turai sun lashi takobin nuna goyon baya ga sabuwar yarjejeniyar da za ta bada damar kafa wasu dokoki kan manhajar da ake amfani da ita wajen kaddamar da hare-hare a shafukan intanet.

Masu fafutukar na fatan kasashen duniya su kauce wa kai farmaki kan kayayyakin more rayuwa da talakawa suna dogara da su musamman a lokutan yaki.
Masu fafutukar na fatan kasashen duniya su kauce wa kai farmaki kan kayayyakin more rayuwa da talakawa suna dogara da su musamman a lokutan yaki. udovic Marin/Pool via REUTERS
Talla

Kasashen sun sanya hannu kan yarjejeniyar samar da wadannan dokokin hana kaddamar da hare-hare a shafukan Intanet a wani zama da suka gudanar a birnin Paris na Faransa a yau Litinin.

Sai dai Kasashen China da Rasha da Amurka ba su raattaba hannu kan yarjejeniyar ba, abin da ke nuna rashin amincewarsu karara da kafa sharuddan amfani da manhajar hare-haren a Intanet da a yanzu ya zama ruwan dare wajen haddasa rikice-rikicen zamani.

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean Yves Le Drian ya ce, ana bukatar samar da sharuddan don kauce wa aukuwar yaki a shafukan Intanet.

Masu fafutuka sun bukaci aiwatar da yarejeniyar yanar gizo ta birnin Geneva wadda ta shinfida sharuddan kaddamar da yake-yaken.

Masu fafutukar na fatan kasashen duniya su kauce wa kai farmaki kan kayayyakin more rayuwa da talakawa suna dogara da su musamman a lokutan yaki.

Ana dai zargin kasashen duniya da dama a samar da manhajar kai hare-haren a shafukan intanet, yayin da a gefe guda ake zargin Rasha da yin kutse a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

A bara dai, irin wannan mummunan kutsen ya gurgunta ayyukan asibitoci da dama a Birtaniya, tare kuma da yin tarnaki a wasu kasashen duniya 150 a cikin sa’oi 24, kuma a wancan lokacin Korea ta Arewa aka zarga da wannan aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.