rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Isra'ila Falasdinawa Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hamas ta sanar da tsagaita wuta da Isra'ila

media
Jiragen yaki na Isra'ila a lokacin da suke ruwan wuta a yankin Gaza REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa

Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta sanar da kulla yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila wadda kasar Masar ta shiga tsakanin bayan kwashe kwana biyu ana fafatawa a tsakanin su.


A yankin,Falasdinawa sun harba makaman roka akalla 460 cikin Israila a cikin kwanaki biyu, abinda ba’a taba gani ba, wanda ya raunana Yahudawa 27, yayin da Israila ta mayar da martani da hare haren sama a wuraren da tace mallakar kungiyar Hamas ne da Islamic Jihad.

Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taro a asirce amma babu wani bayani da akayi a kai.

Jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya bukaci kwamitin sulhu ya dauki nauyin da ya rataya akan ta.