rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Turkiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Saudiya ta yi watsi da bukatar binciken kasashen duniya kan Khashoggi

media
Tuni dai hukumomin Turkiya suka nuna shakku kan matakin na Saudiya. Angela Weiss / AFP

Ministan harkokin wajen Saudi Arabia Adel al-Jubeir ya yi watsi da bukatar Turkiya na gudanar da binciken kasashen duniya kan hallaka Dan Jarida Jamal Khashoggi.


Al-Jubeir ya ce Saudiya na da hukumomin binciken ta kuma ba za ta amince da duk wata bukatar kafa wani kwamitin kasashen duniya ba, domin yanzu haka batu ne na shari’a kuma za’a gabatar da wadanda ake zargi su 5 a gaban kotu domin amsa tambayoyi.

Hukumomin Turkiya sun bayyana shaku kan rahotan binciken da Saudiya ta gabatar wanda ya nesanta Muhammad bin Salman daga zargin ba da umurnin kashe dan jaridar.

Ministan harkokin wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu ya ce babu wani sabon abu da rahotan binciken Saudiya yayi bayani, banda tabbatar da abinda suka sani na kasha Khashoggi da kuma narkar da gawar sa.