Isa ga babban shafi
Saudiya-Turkiya

Babban mai shigar da kara na Saudiya ya nemi kisan makasan Khashoggi

Babban mai shigar da kara na Saudiya ya nemi zartas da hukuncin kisa kan mutane 5 cikin 11 da ake zargi da kisan dan jarida Jamal Khashoggi a Ofishin jakadancin kasar da ke birnin Santanbul na Turkiya ranar 2 ga watan Oktoban da ya gabata.

A cewar ma'aikatar shari'ar Saudiyan, mutanen 5 cikin 11 da yanzu haka ke hannun hukumomi su ne ke da hannu dumu-dumu a kisan fitaccen dan jaridar Jamal Khashoggi.
A cewar ma'aikatar shari'ar Saudiyan, mutanen 5 cikin 11 da yanzu haka ke hannun hukumomi su ne ke da hannu dumu-dumu a kisan fitaccen dan jaridar Jamal Khashoggi. Reuters
Talla

Cikin sanarwarsa wadda Shalaan Al-Shalaan mai magana da yawun ma’aikatar shari’ar kasar ya fitar jiya ta ce bincikensu na nuni da cewa mutanen biyar su ke da alhakin kisan dan jaridar.

Sai dai a wasu kalaman Ministan harkokin wajen kasar Adel Al-Jubeir ya ce Saudiya baza ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta kammala gano wadanda ke da hannu a kisan Khashoggi tare da hukuntasu bisa tanadin doka.

A cewarsa wadanda ake zargin ‘yan saudiya ne haka zalika shima wanda aka kashe dan kasar ne don haka babu wata hujja da za ta sa a bukaci shigowar wasu kasashe cikin binciken dama yanke hukuncin.

Al-Jubeir ya kuma bayyana cewa suna kokarin ganin an fito da gaskiya don kowa ya gani musamman ga masu kokarin mayar da bnatun na siyasa wanda ya bayyana da abin takaici.

Ka zalika Al-Jubeir nesanta Yarima mai jiran gado na Saudiya Muhammad bin Salman da zargin da wasu ke yi na hannunsa a kisan Jamal Khashoggi.

Tuni dai Amurka ta yi maraba da matakin na Saudiya tana mai cewa wani yunkuri ne na wanke kanta tare da tabbatar da adalci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.