Isa ga babban shafi
Amurka-Rasha

Trump ya rubuta amsoshin tambayoyin da ake masa kan Rasha

Shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya rubutawa Robert Mueller da ke bincike kan zargin katsalandan din da Rasha ta yi a zaben kasar amsoshin tambayoyin da ya yi masa.

Tun bayan gano zargin hannun Rasha da yin kutse a zaben kasar ta Amurka, Shugaba Trump ke ci gaba da fuskantar matsin lamba don tabbatar da ko akwai masaniyarsa a katsalandan din na Rasha.
Tun bayan gano zargin hannun Rasha da yin kutse a zaben kasar ta Amurka, Shugaba Trump ke ci gaba da fuskantar matsin lamba don tabbatar da ko akwai masaniyarsa a katsalandan din na Rasha. REUTERS/Jonathan Ernst
Talla

Yayin ganawa da manema labarai a fadar sa, shugaba Trump ya ce yau ya rubuta amsoshin cikin sauki, duk da ya ke bai mikawa mai gudanar da binciken ba.

Shugaban wanda ya bayyana binciken a matsayin zagon kasa, ya ce tun farko ma bai dace ace ana yin sa ba, kuma yana da yakinin ya zo karshe kenan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.