rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Saudiya Amurka Turkiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Amurka zata bayar da goyon baya don zakulo masu hannu a kisan Khashoggi

media
Mike Pence mataimakin Shugaban Amurka Reuters/路透社

Mataimakin Shugaban Amurka Mike Pence a yau asabar ya dau alkawalin gani an zakulo mutanen dake da hannu a kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi ,sanarwa dake zuwa yan lokuta bayan da hukumar leken asirin Amurka ta CIA ta falasa cewa yarima Mohammed Ben Salmane ne ya bayar da umurni na hallaka dan jaridar.


Amurka ta na a shirye don gani an hukunta masu hannu a wannan kazamin aiki a cewar mataimakin shuugaban Amurka Mike Pence.

A cewar jaridar Washington Post hukumar leken asirin ta CIA ta gano sheida ta musaman dangane da tattaunaw ta waya tsakanin Khalid Ben Salmane jakadan Saudiya a Amurka da dan jaridan, wanda ya tabbatar masa da cewa zai iya zuwa ofishin jakadancin Saudiya a Istanbul ba tareda wani sharadi ba.