rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Turkiya Saudiya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hukumar Leken Asiri dake Amurka CIA ta gano Yariman Saudiya na da hannu a kisan Kashoggi.

media
Marigayi Jamal Kashoggi rfi

Hukumar leken asiri dake Amurka CIA ta bankado cewa Yarima mai jiran gado na Saudiya Yarima Mohammed bin Salman ya bada umarnin kashe fitaccen dan jaridan nan na Saudiya Jamal Kashoggi a birnin Santambul na Turkiya.


Kafofin yada labaran Saudiya tun ajiya Juma'a suka yada wannan bincike na Hukumar CIA.

Jaridar Washington Post ta fara yada wannan labari inda take cewa CIA ta gano ‘yan Saudiya 15 da suka tafi Turkiya domin aiwatar da umarnin Yarima Mohammed.

A jiya anyi addu'oi a kasashen duniya ciki har da Saudiya don neman Allah ya gafartawa mamacin.