Isa ga babban shafi
Faransa-Jamus

Macron na neman hadin kan Jamus kan zaman lafiyar duniya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci hadin kan Jamus a yayin jawabinsa game da nauyin da ya rataya akan nahiyar Turai na kare duniya daga afkawa cikin rikice-rikice.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Jamus
Shugaban Faransa Emmanuel Macron a Jamus REUTERS/Fabrizio Bensch
Talla

Mr. Macron na magana ne a birnin Berlin, in da yake halartar bikin shekara-shekera don tunawa da wadanda suka rasa rayukansu a yake-yake.

Shugaban ya shaida wa Majalisar Dokokin Jamus cewa, akwai bukatar karfafa nahiyar Turai musamman saboda aikin da ke gabanta na tabbatar da zaman lafiya a duniya

Macron ya kuma bukaci goyon bayan Jamus wajen kafa rundunar kasashen Turai ta musamman wadda ya ce, za ta takaita dogarar da nahiyar ke yi kan Amurka wajen samar da tsaro.

Kazalika shugaban ya bukaci dora sabbin haraji kan manyan kamfanonin fasahar Intanet.

Shugabar Gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta bayyana goyon bayanta na wucen gadi kan wasu bukatun na Macron, yayin da wasu bukatun ke da sarkakiya a Berlin.

Shugabannin biyu sun gana da juna bayan jawabin na Macron, in da suka tattauna kan batutuwan da suka shafi shige da fice da harkar tsaro da kuma dora harajin kan manyan kamfaofin intanet.

Kazalika ana saran kasashen biyu su sanar da shirinsu na takaita kasasfin kudin kasashen Turai da ke amfani da takardar kudi na Euro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.