Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya-Yanyi

Lokacin daukar matakan gyara kan dumamar yanayi na kurewa - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mummunar iskar da ke gurbata muhalli ta karu sosai a sararin samaniya, daya daga cikin manyan sinadaren da ke haifar da dumamar yanayi.Rahotan Majalisar ya ce lokacin daukan matakan gyara na dada kurewa.

A cewar Majalisar Dinkin Duniya kofar da ake da ita don daukar matakan da suka da ce na kara tsukewa a kowacce rana.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya kofar da ake da ita don daukar matakan da suka da ce na kara tsukewa a kowacce rana. @time
Talla

Yayin da ake shirin gudanar da taron kasashen duniya kan hanyoyin da za’a bi don shawo kan matsalar sauyin yanayi a kasar Poland cikin watan Disamba mai zuwa, Majalisar Dinkin Duniya na kokarin sake janyo hankalin gwamnatocin kasashen duniya wajen ganin sun dauki matakan aiwatar da kudirorin rage ayyukan da ke haifar da dumamar yanayi da kasa da maki 2 a ma’aunin salos ‘celsius’ kamar yadda aka amince a taron Paris na shekarar 2015.

Shugabar kungiyar masu kula da muhalli ta duniya, Petteri Taalas ta ce rashin daukar matakin rage fitar da sinadarin da ke haifar da dumamar yanayi zai yi mummunar illa ga halittun da ke rayuwa a doran kasa.

Jami’ar ta ce kofar da ake da ita na daukar matakan da suka da ce na kara tsukewa a kowacce rana.

Cikin wasikar da Petteri Taalas ta rubutawa shugabar hukumar kare hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet, ta yi gargadi kan illolin da ake fuskanta da ma wanda za  ayi fuskanta nan gaba.

Taalas ta ce kasashen duniya da yanayin da ake amfana da shi, da mutane da kuma hanyar rayuwarsu za su daina wanzuwa muddin aka cigaba da tafiya haka ba tare da daukan matakan da suka dace ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.