Isa ga babban shafi
Chadi-Isra'ila

Idris Deby na Chadi na ziyara a Isra'ila

Shugaba Idris Deby na Chadi ya zama shugaban kasar na farko da ya kai ziyarar aiki Israila inda ya bayyana bude wani sabon babin dangantaka bayan ganawar da ya yi da Firaminista Benjamin Netanyahu.

Karon farko kenan da wani shugaba daga kasar ta Chadi mai rinjayen musulmi ke makamanciyar ziyarar a kasar Isra'ila ta yahudawa.
Karon farko kenan da wani shugaba daga kasar ta Chadi mai rinjayen musulmi ke makamanciyar ziyarar a kasar Isra'ila ta yahudawa. REUTERS/Ronen Zvulun
Talla

Shugaban Chadi Idris Deby wanda ziyarar ta shi ke zuwa a bazata zuwa Isra’ila, ita ce karon farko tun bayan dawowar huldar Diflomasiyya tsakanin kasashen biyu a shekarar 1972 bayan tun farko sun fuskanci baraka tsakaninsu a shekarun a 1967 sakamakon matsin lambar Isra’ilan ga yankin Falasdinu.

A ganawar Idris Deby da Firaminista Benjamin Netanyahu da yammacin yau, shugabannin biyu sun tattauna kan matsalolin da suka shafi tsaro dama ta yadda Isra’ila za ta taimakawa Chadin wajen yakar ayyukan ta’addancin da ta ke fuskanta.

Kasar Chadi mai rinjayen mabiya addinin Islama na daga cikin kasashen yammacin Afrika da yanzu haka ke fuskantar barazanar tsaro, yayin da ko a watan da ya gabata ma sai da ta samu tallafin kayakin yaki dama kudade don fatattakar Boko Haram.

A cewar Netanyahu bayan kammala ganawarsa da Deby a wata tattaunawarsa da manema labarai, lokaci ya yi da za su fadada alaka tsakaninsu da Chadi wadda ke matsayin tsohuwar abokiyar huldarsu.

Ana dai ganin matakin baya rasa nasaba da kokarin Netanyahu wajen ganin ya gyara alakar da ke tsakaninsa da kasashen yankin Gulf dama kasashen da ke da rinjayen musulmi bayan takaddamar data kunno kai game da yankin gaza wadda ta haddasa rarrabuwar kawuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.