rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Ukraine

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen duniya sun bukaci Rasha ta saki jiragen ruwan Ukraine

media
Tuni dai kasashen duniya suka yi tir da matakin na Rasha wanda suka ce ya ketare iyaka. REUTERS/Pavel Rebrov

Kasashen Ukraine da Rasha sun dukufa wajen lalibo hanyoyin warware takadamar tsawon shekaru a tsakaninsu, inda mahukunta a Kiev da abokan kawancensu na kasashen yammaci, suka bukaci Rasha da ta sallami jirgen ruwan ukrain da jami’an tsaron gabar ruwanta suka kama a kan ruwan yankin Crimea da ke karkashin ikon Rasha.


A cewar kakakin fadar Kremlin ra Rasha Dmitri Peskov, Rasha ta kare matsayinta da cewa, ta yi haka ne a karkashin dokokin duniya, bayan da ta zargi jirgen ruwan na Ukraine da shiga farfajiyar Ruwan kasar ta.

A marecen jiya lahadi ne jiragen dakarun tsaron gabar ruwa Rasha suka killace wasu jiragen ruwan kasar Ukraine 3, bayan da suka yi harbe harbe a kansu da suka yi sanadiyar jikkatar fasinjojin da ke cikin jiragen da dama, wadanda suka hada da yan Ukraine 6 a cewar Kiev, 3 a cewar mahukumtan Masco, al’amarin da ya haifar da matukar bacin rai ga kasashen yammaci aminan kawance Ukraine.

Sai dai kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani taron gaggawa da kasashen 2 suka bukata yau Litinin, a yayinda Kungiyar tsaro ta Nato ta bayyana shiga wani taron gaggawa tare da Ukraine duk a yau Brussels domin sanin matakin dauka.

Tuni dai kakakin ma’aikatar harakokin wajen Faransa ya bayyana cewa babu wata hujja da Rasha za ta gabatar na dalilinta na amfani da karfin soja kan jiragen ruwan kasar ta Ukraine.

A yayinda a nasa bangaren shugaban majalisar dokokin Kungiyar tarayyar turai, Donald Tusk, ta shafinsa na Twitter " yayi tir da amfani da karfin da dakarun na Rasha suka yi.