rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Argentina Saudiya Turkiya Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Human Rights Watch ta bukaci kame Muhammad bin Salman a Argentina

media
Sai dai kawo yanzu babban alkalin kasar ta Argentina Ariel Lijo, da kuma ofishin babban mai gabatar da kara ba su ce komai ba dangane da bukatar da Human Rights Watch duk da cewa sun karbe ta rubuce. Bandar Algaloud/Courtesy of Saudi Royal Court/Handout/Reuters

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch, ta bukaci gwamnatin Argentina, ta yi amfani da damar da kundin tsarin mulkinta ya bayar, wajen kama Yarima Muhammad bin Salman na Saudiya bisa alakarsa, da kisan dan jaridar kasar Jamal Kashoggi, da kuma aikata laifukan yaki a Yemen.


Babbar darakatar kungiyar ta Human Rights mai kula da yankin gabas ta tsakiya da kuma arewacin Afrika Sarah Leah Whitson ta ce sun dauki matakin mika bukatar ga gwamnatin Argentina ne, la’akari da cewa Yarima Muhammad Bin Salman, zai halarci taron kungiyar kasashen G20 a wannan mako da zai gudana a Buenos Aires, babban birnin kasar ta Argentina.

Kundin tsarin mulkin Argentina dai ya bai wa hukumomin tsaron kasar damar kama duk wanda ake zargi da aikata laifukan yaki, da suka hada da azabtarwa, da kuma kisan gilla, domin bincikarsa, ba tare da la’akari da inda aka aikata laifukan ba.

Sai dai kawo yanzu babban alkalin kasar ta Argentina Ariel Lijo, da kuma ofishin babban mai gabatar da kara ba su ce komai ba dangane da bukatar da Human Rights Watch duk da cewa sun karbe ta rubuce.

Kisan gillar da aka yi wa dan jarida Jamal Kashoggi a ofishin jakadancin Saudiya da ke Turkiya makwanni 6 da suka gabata, ya raunana dangantakar Saudiyan da kasashen duniya da dama, zalika ya rage kimar mai jiran gadon sauratar kasar ta Saudiya, Yarima Muhammad Bin Salman.