rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka China Rasha Saudiya Turkiya Faransa Argentina

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taron G20 ya kankama a Buenos Aires na Argentina

media
Kasashen 20 hade da kasashen da suka gayyata sun hallara a birnin na Buenos Aires don fara tattaunawa a taron wana zai tabo batutuwa da dama. REUTERS/Marcos Brindicci

Yau Juma'a kasashe 20 na duniya mafiya karfin tattalin arziki sun kammala hallara a birnin Buenos Aires na Argentina don fara taron da suka saba gudanarwa wanda ke da nufin tabo kalubale daban-daban da sassan duniya ke fuskanta musamman ta fuskar tattalin arziki.

 


Batutuwa masu alaka da rikicin kasuwanci, matsalar dumamar yanayi, da kwace jiragen ruwan Ukraine da ma dambarwar baya-bayan nan kan kisan dan jarida Jamal Kashoggi su ne za su mamaye taron wanda zai kankama a gobe Asabar.

Sai dai kuma a gefe guda hankulan za su sake komawa kan ganawar da ake sa ran za ta gudana tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na China Xi Jinping, bayan da shugaban na Amurka ya soke ganawa da Putin na Rasha.

Akwai dai fargabar cewa ba lallai kasashen China da Amurka su iya cimma wata kwakkwarar yarjejeniya don kawo karshen yakin kasuwancin da ke tsakaninsu ba.

A bangare guda Putin na Rasha ya ce zai gana da Yarima mai jiran gado na Saudiya don samun karin haske game da kisan dan jarida Jamal Khashoggi.

Tuni dai shuagban Faransa Emmnuel Macron ya yi gargadi kan kada taron na G20 ya koma kafar rura rikici maimakon haduwa don lalubo hanyoyin da za a magance matsalolin da duniya ke fuskanta.