Mueller ya ki bada shawarar daure Janar Michael Flynn
Jami’in Bincike na musamman kan zargin katsalandan da ake yiwa Rasha wajen zaben Amurka Robert Mueller yaki bada shawarar daure tsohon mai baiwa shugaba Donald Trump shawara kan harkokin tsaro Janar Michael Flynn saboda hadin kan da ya baiwa masu bincike a baya.
Wallafawa ranar:
Mueller yace Flynn wanda a bara ya amsa cewar yayi karya kan tuntubar wakilan Rasha jim kadan bayan zaben Trump a shekarar 2016, ya taimaka wajen binciken da ake masa da ma wasu daban, wajen ganawar da akayi da shi har sau 19.
Takardar da Mueller ya gabatarwa kotu tace duk da kuskuren da yayi, ya bada gagarumar rawa wajen aikin soji da ya kai mukamin Janar da kuma zama shugaban leken asiri a ma’aikatar tsaro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu