Isa ga babban shafi
Majalisar Dinkin Duniya - Morocco

Yarjejeniyar kariya ga baki masu kaura ta samu sa hannun kasashe 150

Taron Majalisar Dinkin Duniya kan yadda za a inganta kula da bakin da ke kaura tsakanin kasashe a Morocco ya amince da wani shiri a gaban shugabannin da wakilan kasashe kusan 150 duk da janyewar da wasu kasashe suka yi.

Shirin a cewar Gutteress shi ne hanya daya tilo da zai bayar da kariya ga daukacin 'yanciranin da ke kaura a sassan duniya.
Shirin a cewar Gutteress shi ne hanya daya tilo da zai bayar da kariya ga daukacin 'yanciranin da ke kaura a sassan duniya. REUTERS/Gonzalo Fuentes/Pool
Talla

Ita wannan yarjejeniya da wakilan kasashe kusan 150 suka amince da ita a Marakesh da ke Morocco, an yi mata lakabi da shiri na musamman domin kare baki da tabbatar da tafiyar su cikin yanayi mai kyau, wanda aka kamala tantance shi bayan tarurrukan da aka kwashe watanni 18 ana yi.

Yarjejeniyar ta gindaya sharidodi 23 na samun halartacciyar kaura da kuma haramta ketare iyaka ba tare da bin ka’ida ba, ganin adadin bakin da suka kaura ya zarce miliyan 250 yanzu haka.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterress ya bayyana yarjejeniyar samar da kariyar ga bakin hauren a matsayin mafita guda da za ta kawo karshen kalubalen da 'yan ciranin kan fuskanta.

Guterres ya ce abin kunya ne asarar rayukan da ake samu musamman akan hanyar bakin hauren ta yin kaura zuwa nahiyar Turai don samun ingantacciyar rayuwa.

Cheryll Pareira, wata yar assalin Sri Lanka da ta yi kaura zuwa Canada, wadda kuma ta gabatar da jawabi gaban taron, ta bayyana fatar tabbatuwar shirin don bayar da kariya ga dimbin bakin da ke kaura.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.