Isa ga babban shafi
Amurka

Kotun Amurka ta daure Michael Cohen shekaru 3 a gidan yari

Tsohon Lauyan shugaba Donald Trump na Amurka Michael Cohen ya cacaki tsohon mai gidan na sa bayan ta kotu ta daure shi shekaru 3 a gidan yari saboda samun sa da laifin laifuffukan da suka hada da biyan wasu mata biyu kudade saboda mu’amala da shugaban.

Michael Cohen tsohon lauyan Donald Trump wanda bai nemi sassaucin kotu a hukuncin da ta yanke masa ba, ya ce sai yanzu ya ji sanyi a ransa tun bayan fara aiki ga shugaban na Amurka.
Michael Cohen tsohon lauyan Donald Trump wanda bai nemi sassaucin kotu a hukuncin da ta yanke masa ba, ya ce sai yanzu ya ji sanyi a ransa tun bayan fara aiki ga shugaban na Amurka. REUTERS/Andrew Kelly
Talla

Cohen ya ce hakkin sa ne ya kare ayyuka marasa kyau da Ubangidan sa ya yi, yayin da ya ke amsa laifi a gaban alkali William H Pauley III.

Lauyan bai nemi kotu ta yi masa ahuwa ba, bayan ya amsa laifin kaucewa biyan haraji da yi wa hukuma karya da karbar kudaden kamfe ta hanyar da bai kamata ba da kuma yaudarar Majalisa.

Bayan yanke hukuncin Cohen ya ce yau ya samu yancin kan sa, domin tun bayan amincewa ya yi wa attajiri (Trump) aiki ya ke zama cikin ukuba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.