rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Poland Canjin Yanayi Muhalli

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wakilan kasashe sun cimma matsaya kan tunkarar dumamar yanayi

media
Yadda hayaki ke fita daga masana'antar Belchatow mai amfani da makamashin Kwal mafi yawa a nahiyar turai, da ke kasar Poland. 28/11/2018. ©REUTERS/Kacper Pempel

Wakilan kasashe akalla 200 dake halartar taron rage dumamar yanayi a Poland, sun cimma matsaya kan matakan da za’a bi wajen soma aiwatar da yarjejeniyar tunkarar matsalar daga shekara ta 2020, wadda aka rattabawa hannu a Paris cikin shekarar 2015.


Banbancin ra’ayi kan batun makomar kasuwar makamashin kwal na daya daga cikin, batutuwan da suka kusan haddasa wani karin tsaiko ga kammala taron.

Sai dai daga bisani an cimma matsaya kan kudrin na kowace kasa ta cika alkawarin zaftare kaso mai tsoka na amfani da makamashin, wanda ke taka rawa kan karfafa matsalar ta dumamar yanayi.

Taron na Katowice babban birnin Poland ya kuma amince da bukatun kasashen masu tasowa da matsalar tafi cutarwa, kan tallafin da aka alkawarta basu.

Sauran batutuwan da aka gaza cimma matsaya guda kansu a baya, sun kunshi, yadda za’a samar da kudaden aiwatar da shirin na rage dumamar yanayin, da kuma kasashen da ya kamata su samar da kaso mafi tsoka daga cikin tallafin.