rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Vatican

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Bukukuwan Kirismeti a sassan duniya

media
Shugaban cocin Kinshasa, Fridolin Ambongo Besungu, ranar 24 disamba 2018 JOHN WESSELS / AFP

Kiristoci a sassan duniya na gudanar da bukukuwan kirismeti domin tunawa da zagayowar ranar haihuwar Yesu Almasihu, inda aka gudanar da addu’o’i a muhimman wurare da suka hada da Bethleem, Jerusalem, Vatican da ma sauran mujami’o’i a daren da ya gabata.


A garin Bethlehem da ke cikin Palesdinu inda aka haifi Yesu Almasihu, dubban mutane ne suka taru domin raya daren  jiya ta hanyar addu’o’I da kuma nuna farin ciki.

Wani lokaci a yau kuwa shugaban mabiya darikar Katolika a duniya Paparoma Francis zai jagoranci addu’o’I na shekara-shekara tare da gabatar da jawabi zuwa ga mabiya a sassan duniya, domin bayyana muhimmancin wannan rana da kuma sakon da kunshe a cikinta.