rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Ukraine

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Rasha ta fadada takunkumanta kan Ukraine

media
Kawo yanzu dai fiye da mutane 500 takunkuman na Rasha ya shafa a Ukraine. REUTERS/Maxim Shemetov

Rasha ta sanar da matakin fadada takunkuman karya tattalin arzikin da ta sanya wa Ukraine, matakin da yanzu takunkumin zai shafi kusan mutane 250 baya ga bangarorin kasuwanci da kamfanonin kasar.


Cikin jawaban Firaminista Dmitri Medvedev ya wallafa a shafinsa na Twitter da yammacin yau Talata, ya ce akwai mutane 245 da takunkumin zai shafa sai kamfanoni 7 galibi wadanda suka shafi makamashi da kera-kere dukkaninsu takunkuman zai shafe su kai tsaye.

Tun bayan farawar tsamin alaka tsakanin Moscow da Kiev a cikin watan Nuwamba kawo yanzu akalla mutaen 567 baya ga kamfanoni 75 takunkuman na Rasha ya shafa.