Isa ga babban shafi
Brazil

Bolsonaro, ya sha alwashin yakar matsalolin cin hanci da rashawa a Brazil

Sabon shugaban Brazil da aka rantsar a yau talata Jair Bolsonaro, jim kadan bayan kammala bikin rantsuwar ya sha alwashin yakar matsalolin cin hanci da rashawa da kuma na yawaitar kisan gilla da ‘yan kasar ke fama da su.Bolsonaro mai ra’ayin rikau, ya sha alwashin aiki babu dare ba rana, wajen tabbatar da ci gaban Brazil.

Jair Bolsonaro sabon Shugaban kasar Brazil
Jair Bolsonaro sabon Shugaban kasar Brazil REUTERS/Ricardo Moraes
Talla

Sabon shugaban, ya soma aiwatar da shirin sassauta dokokin mallakar bindiga a kasar, kamar yadda ya yi alkawari a baya, matakin da ya ce, zai taimakawa ‘yan kasar na gari wajen kare rayukansu.

Wata kididdigar bankin duniya ta ce, Brazil ce kasa ta 8 a duniya da aka fi kisan kai, yayin da, hukumomin tsaron kasar suka ce a shekarar 2017 an aikata kisan gilla dubu 63 da 883 a fadin kasar.

Shugaban kasar Jair Bolsonaro da tsohon kaftin din sojin Brazil mai ra’ayin rikau, Jair Bolsonaro ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen makon watan Oktoba na shekara ta 2018, in da ya doke abokin takararsa Fernando Haddad da sama da kashi 55 na kuri’un da aka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.