Isa ga babban shafi
Faransa

Masu bore sun bige da bikin sabuwar shekara a Faransa

Miliyoyin al’umma a sassan duniya sun gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekarar 2019, in da a Faransa dubun-duban jama’a da suka hada da masu zanga-zangar adawa da gwamnati suka yi dandazo a Champs Elysees da ke birnin Paris don gudanar da bikin cikin lumana da kuma matakan tsaro.

Masu zanga-zangar sanye da riguna launin dorawa sun ce, lokaci ne na nuna murna amma na zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa ba
Masu zanga-zangar sanye da riguna launin dorawa sun ce, lokaci ne na nuna murna amma na zanga-zangar adawa da gwamnatin Faransa ba reuters
Talla

Faransawa da masu yawon bude ido sun shaida wasan tartsatsin wuta a Champs Elysees mai dauke da wuraren kayatarwa jim kada da shiga sabuwar shekarar ta 2019, yayin da aka girke jami’an tsaro kimanin dubu 147 a sassan kasar.

Masu zanga-zangar adawa da matakin gwamnatin Faransa na tsauwala kudin haraji sanye da riguna launin dorawa, sun saje da masu bikin na sabuwar shekara, kuma a wannan karo ba su haifar da wani cikas ba saboda a cewarsu lokaci ne na nuna murna a daukacin Faransa.

Tun a cikin watan Nuwamban da ta gabata ne, masu rigunan launin dorawar, suka fara zanga-zanga a sassan Faransa, abin da ya haifar da arangama tsakanisu da jami’an ‘yan sanda har aka samu asarar tsirarun rayuka.

A yayin gabatar da jawabin shiga sabuwar shekarar, shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya ce, masu zanga-zangar ba za su tilasta wa gwamnatinsa jingine tsare-tsarenta na tattalin arzikin kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.